IQNA

Za A Bude Masallatai A Saudiyya  Banda Na Makka

23:58 - May 26, 2020
Lambar Labari: 3484839
Tehran (IQNA) sarkin kasar Saudiyya ya bayar da umarnin bude masallatai a biranan kasar amma banda masallatan birnin Makka.

Shafin yada labarai na arabi 21 ya bayar da rahoton cewa, sarkin kasar Saudiyya Salman Bin Abdulaziz ya bayar da umarnin bude masallatai a biranan kasar, tare da kiyaye ka’idoji na kiwon lafiya, amma hakan ba zai shafi masallatan birnin Makka ba.

Wannan umarni zai fara aiki ne daga ranar Lahadi mai zuwa tsawon kwanaki 20, daga lokacin kuma za a dauki mataki na gaba, kan ci gaba da barin masallatan a bude ko kuma sake rufe su.

Haka nan kuma za a janye dokar hana halartar wuraren ayyukan gwamnati, da na kamfanoni masu zaman kansu, amma hakan shi ma zai gudana ne bisa tsatsare na ma’aikatar kiwon lafiya.

Baga haka kuma sarki ya bayar da umarnin bude hanyoyi domin zirga-girga a tsakanin biranan kasar na wasu kayyadaddun lokuta, kamar yadda kuma za a sassata dokar zirga-zirgar jama’a a cikin birane na wasu sa’oi a cikin rana.

Kimanin mutane dubu 75 ne suka kamu da cutar corona a kasar Saudiyya, yayin da 399 daga cikinsu suka rasa rayukansu.

 

 

3901306

 

 

 

captcha